Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Nijar mazauna Amurka na fatan a yi zaben zagaye na biyu lafiya


Kasar Nijar
Kasar Nijar

Yayinda da zaben shugaban kasar Nijar zagaye na biyu ke karatowa 'yan Nijar mazauna nan Amurka sun bayyana ra;ayinsu

Fatan 'yan Nijar dake zaune a nan Amurka shi ne a yi zaben lami lafiya ba tare da tada hankali ba ko kawo wanta tashin tashina.

Sun kira masu takara da su kai zuciyarsu nesa su rungumi sakamakon zaben domin Allah ne ke ba mutum mukami.

Dangane da matasa su ma an kirasu kada su yadda a yi anfani dasu a mayar dasu 'yan banga. 'Yan siyasa abun da zasu ci suke nema. Bayan zaben za'a gansu tare. Saboda haka yadda suka tabbatar da zaman lafiya a zagayen farko su sake dagewa su tabbatar babu tashin hankali.

Siyasar kabilanci ba zata yi tasiri a kasar Nijar kuma duk wanda ya yi kokarin yin anfani da kabilanci zai ji kunya. 'Yan Nijar daya suke babu banbanci.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:02 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG