Dandalin Taksim dake birnin Istanbul, wanda kuma babbar jam’iyyar adawa ta Republican Peoples Party ta hada, Inda suka hadu da sauran jam’iyun siyasar kasar, ciki harda jam’iyyar shugaban kasa Tayyip Erdogan ta Islamic Justice wadda ta mulki kasar tun shekara ta 2002.
Wani al'amarin kuma na bayyana hadin kan 'kasa ya fito daga Shugaban Rundunar Sojojin Sama na Turkiyya, wadda ta fitar da wata takarda mai ban mamaki, da ke jaddada goyon baya ga Hafsan Hafsoshin Soji, Hulusi Akar.
Wasu daga cikin rundunar sojan sama na daga cikin sojojin da suka yi kokarin juyin mulkin, lokacin da aka yi garkuwa da Akar.
Shugaban kasa Erdogan, wanda ya kauce ma kamu da yiwuwar kisa, ya ayyana dokar ta baci a kasar, wadda zata ba shi damar aiwatar da doka ba tare da amincewar ‘yan majalisa ba, a kokarin neman duk wadanda ke da hannu a juyin mulkin, wanda akalla mutane 246 suka rasa rayukansu ciki, wasu sama da 2000 suka raunata.