Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yaron Da Ya Kashe Mutane a Munich Bajamushe Ne Dan Asalin Iran


'Yan Sanda a Munich ta Jamus a Shirin Ko Ta Kwana a Jiya Juma'a Bayan Wani Ya Kashe Jama'a.
'Yan Sanda a Munich ta Jamus a Shirin Ko Ta Kwana a Jiya Juma'a Bayan Wani Ya Kashe Jama'a.

‘Yan sanda a Jihar Bavarian da ke Jamus, sun ce Bajamushen-Ba'Iraninyen yaron nan dan shekaru 18 da ya kashe mutane 9 tare a wani rukunin shaguna da ke birnin Munich, ba shi da wata alaka da kungiyar ISIS ya zuwa yanzu.

Jami’an sun ce sun bincike muhallinsa tsaf amma ba wata alamar da aka samu da ke alakanta shi da kungiyar ‘yan ta’addar na ISIS.

Maimakon haka sun alakanta kisan da abin nan ake cewa harbin bajinta kan mai uwa da wabi.

Domin kuwa an sami wani littafi a dakinsa mai suna Rampage on my mind – Why Students Kill. Wato littafin da ke nuna kisan dalilan yin kisan fusata ko makamantansa da dalibai ke yi.

Yaron Bajamushe ne dan asalin kasar Iran wanda aka haifa ya kuma girma a birnin na Munich.

Bayan ya hallaka mutanen 9 ne kuma a ranar juma’ar ya harbe kansa. Har yanzu dai ba bayanin ko me yasa wannan yaron fusatar da ya hallaka jama’a da kuma kansa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG