Inda ya mika jawabinsa ga dimbin jama’ar da suka taru a birnin Miami na jihar Florida. Tim yayi bayani mai karfi da shiga jikin masu sauraronsa, a lokacin da yake magana yana hadawa da yaren Sifaniyanci kai kace yarensa ne na haihuwa, alhali koya yayi.
Kaine dai tsohon dan jam’iyyar Democrat ne wanda ya bayyana kansa a matsayin gundura, to amma yana da sassaucin ra’ayi, kuma ana kallonsa a matsayin wanda ke da kwarewar da zai iya canza ra’ayin masu zabe su guji Trump su zabi Hillary.
Sanata Tim yana da kima sosai a idon jama’a, sannan ya jaddada cewa bai taba faduwa zabe ba tun da ya fara siyasa, kama tun daga zamansa Magajin Gari Richmond har zuwa zamansa gwamnan jihar Virginia da kuma zamansa Sanata.
Hillary ta kara da cewa, Tim yana cikin Sanatocin da na sani da suke da matukar kima a idanun jama’ar Amurka. Kamar yadda ta fadawa gidan talbijin na CBS.
Tim haifaffen jihar Minnesota ne, ya kuma yi karatun aikin Lauya a Jami’ar Harvard, jami’ar da ita ta haifar da Lauya Barack Obama da a yanzu haka ya ke shugabancin Amurka.