Kamar yadda wata kungiyar rajin kare hakkin dan Adam mai suna Observatory for Human Rights ta bayyana.
Tace asibitoci hudu daga cikin biyar din suna yankin birnin Aleppo ne, da kuma wani guda daya a Atareb da ke yammacin babban birnin.
Dakarun gwamnatin Syria hade da sojojin taron dangi sun yiwa birnin Aleppo kawanya tun makon da ya gabata, garin da shekaru hudu kenan ana jani in jaka tsakanin sojojin gwamnati dana ‘yan tawayen kasar.
Wannan lamarin ya haifar da karancin abinci ga fararen hula mazauna wuraren da ke makale a hannun ‘yan tawaye.
Ga kuma rahoton ma’aikatar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya tace Syria itace ta fi kowace kasa zamewa ma’aikatan lafiya hatsarin shiga don kai dauki.