Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan Amurka kuma dan jami’iyar Republican Mitch McConnel, ya shirya kada kuri’a yau Litinin da rana a kan kawo karshen rufe ma’aikatun gwamnatin Amurka.
Wakilan Majalisar Dokokin zasu kada kuri’a ne a kan tallafawa ma’aikatun gwamnati zuwa akalla makwanni uku nan gaba.
Shugabannin bangarorin biyu na Majalisar sun kwashe dukkan ranar jiya Lahadi suna ganawa kuma suna tattaunawa a kan hanyar kawo karshen takaddamar bakin haure da yayi sanadin rufe wasu ma’aikatun gwamnati.
Sai dai ba’a tantance irin ci gaban da ake samu a tattaunawar ba..
Tunda farko a jiya Lahadin, wakiliyar jihar Maine Susan Collins, mai sassaucin ra’ayi ‘yar jam’iyar Republican tace akwai wakilai takwarorin aikin ta 22 da suka himmantu wurin warware wannan matsala.
Majalisa ta tabbatar da kasafin kudin gudanar da ayyukan gwamnati a karshen makon jiya.
Amma ‘yan jami’iar Democrat a Majalisar sun ki amincewa da kasafin kudin, kuma suna bukatar a kare bakin hauren da aka shigo da su Amurka tun suna yara kanana da bisa ka’ida ba da kae kiransu Dreamers
Su kuwa bangaren jami’iyar Republican sun ce ba zasu tattauna a kan batun bakin haure ba har sai gwamnai ta fara aiki.
Facebook Forum