Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan 'Yan Afirka Dake Zuwa Amurka Ta Barauniyar Hanya Ya Karu


Adadin bakin haure ‘yan kasashen Afrika da hukumar kula da shige ta Amurka ta kama sun karu. A shekarar da ta gabata an kama mutane kasa da dari, amma a ‘yan makonnin da suka gabata, yawan mutane da aka kama sun haye mutane 600.

Tawagar ta bakin haure ‘yan Afrika wani bangare ne na mutanen da ake kamawa wadanda ba ‘yan kasashen Mexico da Amurka ta tsakiya ba ne dake tsallakowa zuwa cikin Amurka ta barauniyar hanya batare da izini ba.

Duk da cewa mafi yawan bakin hauren da ake kamawa suna shigowa ne daga kasashen El Salvador da Guatemala da Honduras, yawan sauran wadanda kuma suke fitowa daga wasu kasashe na daban, ya haye kashi 4 cikin 100 na jimillar mutane kimanin 303,961 da aka kama a shekarar 2017.

A wannan shekarar da muke ciki ta 2019 mutane 593,507 aka cafke, kuma mafiyawansu sun fito ne daga kasashen Angola da Kamaru da jamhuriyar Kongo da Nijar da Najeriya da kuma Somaliya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG