Sai dai shugaban a wannan lokaci yaje kan iyakar ne tare da wata tawagar sanatoci, domin su ga irin yanayin da ake ciki a wurin.
‘Yan majalisar da suka hada da ‘yan Democrats 12 da wani dan independent daya, sun ziyarci iyakar dake McAllen a jihar Texas inda ake yawan gudanar da harkoki da kuma sintirin jami’an tsaro, inda hukumomi suka tsare mutane dake kokarin shigowa kasar a cikin aikinsu.
Wata sanarwar da ofishin shugaban Democrats a majalisar dattawa Chuck Schumer ya fitar na cewa tawagar da isa da safiyar jiya Juma’a ne tare da shugaban hukumar tsaron cikin gida Kevin McAleenan domin bincike da duban iyakar tare da tantance halin da ake ciki a kan iyakar kudancin kasar.
Sanata Chuck Schumer yace tawagar taga wani matsuguni mai kyau a ziyarar wuni daya da ta kai wanda wata kungiyar taimako ta Katolika ke gudanar da ita.
Facebook Forum