Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Na Fuskantar Matsanancin Yanayin Zafi


Kwararru a fannin yanayi sun ce, a wani dan lokaci, yanayin zafin a birnin Washington gundumar kwalambiya, zai kasance kamar na yankin hamadar Death Valley na jihar California mai matsanancin zafi.

Yawancin yan kunan Amurka na fuskantar matsanancin yanayin zafi yanzu haka.

A arewa maso gabashi da tsakiyar yammacin kasar, yanayin a ma’aunin gwaji ya riga ya hau sosai, kuma ana sa-ran zai iya karuwar da ba’a taba gani ba a cikin karshen makon nan. An riga an gargadi jama’a akan su yawaita shan ruwa a lokacin.

Sai dai kwararru a fannin hasashen yanayi sun ce Amurkawa sama da miliyan 87 ke zama yankunan da ta yiwu yanayin zai tsananta zuwa ranar Asabar.

Ana sa ran yanayin zafin a Washington DC, babban birnin kasar zai kai maki 43.3 a ma’aunin Celsius.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG