Gwamnatin Amurka ta sanya takunkumi akan babban kwamandan sojin Myanmar, Min Aung Hlaing da wasu manyan shugabannin sojin kasar, saboda “kisan kiyashin" da aka yi wa musulmi ‘yan kabilar Rohingya a jihar Rakhine da ke arewa maso gabashin kasar.
Takunkumin da aka sanya wa Min Aung Hlaing, da mataimakinsa, Soe Win, da wasu shugabannin biyu da iyalansu, zai hana su shiga Amurka.
Ma’aikatar harkokoin wajen Amurka ta ce, wannan sanarwar ta sa Amurka ta zama kasa ta farko da ta dauki mataki akan manyan shugabannin sojojin kasar ta Burma.”
Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo ya ce, “wani babban misali na rashin nuna adalci hukumomin sojan suka nuna, shi ne, yadda bayanai suka nuna cewa Min Aung, ya ba da umurnin a saki sojojin da aka samu da laifin aikata kisan kiyashin akan ‘yan kabilar ta Rohingya.
Facebook Forum