Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rundunar ‘Yan Sandan Abuja Za Ta Yi Dirar Mikiya Kan Ababen Hawan Da Basu Da Lamba


Nigeria Police Force Logo
Nigeria Police Force Logo

Haka kuma za a aiwatar da tanade-tanaden dokokin rufe lamba da kuma ta amfani da gilashi mai duhu.

A wani yunkuri na dakile karuwar laifuffukan satar mutane da motoci, rundunar ‘yan sandan birnin tarayyar Najeriya (Abuja) tace zata fara kamen ababen hawan da basu da lamba da wadanda keda lamba daya tak, da kuma wadanda lambobin suka kode.

Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a birnin a yau Talata, tace zata tura karin jami’ai da kayan aiki domin yin sintiri da kafa shingayen bincike da kuma kara aikin sanya idanu a fadin birnin tarayyar.

SP Josephine Adeh
SP Josephine Adeh

Haka kuma za a aiwatar da tanade-tanaden dokokin rufe lamba da kuma ta amfani da gilashi mai duhu.

“Muna yabawa juriya da hadin kan da al’umma suke bamu yayin aiwatar da wadannan ayyuka, kuma muna baiwa masu ababen hawa shawara akan su tabbatar da kiyaye wadannan ka’idoji.

“Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja ta dukufa wajen tabbatar da birnin mai cike da tsaro. Muna kuma karfafa gwiwar mazauna birnin akan su kai rahoton duk wani abun da basu yarda dashi ba, tare da baiwa jami’anmu hadin kai.

“Lafiyarku ita ce burinmu,” a cewar sanarwar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG