Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kananan ‘Yan Kasuwa Sun Nemi A Janye Na'urar Tantance Kudaden Harajin TVA A Nijar


Bazoum Mohamed
Bazoum Mohamed

A Jamhuriyar Nijar, kananan ‘yan kasuwa sun bukaci hukumomin kasar su sake tunani a game da sabon tsarin biyan kudaden harajin na TVA da suka shimfida a farkon shekarar nan ta 2022.

Tsarin na nufin dole ne daga yanzu kowane dan kasuwa ya yi amfani da wata na’ura wajen buga takardar saye da sayarwa ta yadda za a tantance zahirin kudaden harajin

da ya kamata ya zuba a ma’aikatar haraji.

A tasu fahimtar biyan wannan haraji a yayin fiton kaya a ma’aikatar costum ita ce hanya mafi dacewa da yanayin kasar ta Nijar.

Rashin sanin kan na’urar da za a yi amfani da ita wajen tantance kudaden harajin TVA da ya wajaba kowane dan kasuwa ya biya daidai da bayanan dake rubuce a takardar saye da sayarwa wato ‘facture certifiee’ ya sa kananan ‘yan kasuwa kiran mahukunta su sake duba wannan tsari da suke yiwa kallon maras dacewa da yanayin kasar Nijer, a bisa la’akari da jahilcin jama’a kamar yadda suka bayyana a taron manema labaran da suka kira Malan Adamou Sama’ila na mai magana da yawun kananan ‘yan kasuwa.

A cewarsu biyan kudaden harajin na TVA ta hanyar ma’aikatar Costum ita ce hanya mafi a’ala da za ta basu damar safke wannan nauyi.

Kafin ta soma zartar da wannan sabon tsari ma’aikatar haraji ta bayyana matakin a matsayin wata hanyar toshe kafar da wasu ke amfani da ita wajen kewayewa hanyoyin biyan haraji to amma a cewar kananan ‘yan kasuwa suna da fargaba akan abinda zai biyo bayan dorewar wannan tsari.

A baya an sha kai ruwa rana a tsakanin kungiyoyin ‘yan kasuwa da hukumomin kula da sha’anin haraji dangane da wannan mataki da ke hangen kawo karshen satar haraji sai dai tuni wasu ‘yan kasuwa suka fara fakewa da wannan sabon tsari wajen tsauwala farashin kayayaki musamman ababen masarufi.

XS
SM
MD
LG