Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Janar Ali Seybou Ya Rasu


Janar Ali Seybou Ya Rasu
Janar Ali Seybou Ya Rasu

Fadar shugaban Nijar ta ayyana zaman makokin kwanaki uku domin jimamin mutuwar Janar Ali Seybou, jigon mulkin dimokuradiyya a kasar

Fadar shugaban Jamhuriyar Nijar ta bayar da sanarwar rasuwar tsohon shugaban kasar Ali Saibou, jiya litinin a Niamey, babban birnin kasar.

Wata sanarwar shugaba Mahamadou Issoufou da aka karanta a gidan telebijin na kasar, ta bayyana jimamin mutuwar, ta kuma ayyana zaman makoki na kwanaki uku a fadin kasar domin tunawa da marigayi janar Ali Saibou.

An kuma ce za a yi masa jana’iza a kauyensu mai suna Dingajibanda a yankin yammacin kasar ta Nijar.

A shekarar 1987, majalisar sojojin dake mulkin Nijar ta zabi Saibou domin ya gaji janar Seyni Kountche, wanda ya rasu a sanadin cutar sankara. A shekarar 1989, a matsayinsa na shugaban jam’iyyar siyasa kwaya daya tal da aka amince da ita, Janar Saibou ya tsaya ya lashe zabe da kashi 99 da rabi cikin 100 na kuri’un da aka kada.

Amma kuma shekaru biyu bayan wannan, shugaba Ali Saibou ya sauyab alkibla, ya bayarda umurnin gudanar da taron muhawara na kasa, taron da ya shimfida mulkin dimokuradiyya a kasar.

Ya sauka daga mulki a shekarar 1993, kuma tun saukarsa ya tsame hannunsa baki daya daga dukkan harkokin siyasa a kasar. Marigayi Ali Seybou, ya bar duniya yana da shekaru 71 da haihuwa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG