Yan hisba a jihar Kano sun damke wasu 'yan mata guda dari da ashirin 120, da ake zargi da karuwanci a wani wurin shakatawa. An gudanar da samamen ne da hadin gwiwar jami'an yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) reshen jihar Kano, wanda suka cafke wasu matasa talatin da bakwai 37, da aka zargi da mu'amula da miyagun kwayoyi.
Da yake wa manema labarai jawabi, babban shugaban kungiyar hisba, Alhaji Abba Sa'idu Sufi, ya bayyana cewa ashirin 20, daga cikin 'yan matan 120, da aka kama kananan yara ne da shekarunsu ke tsakanin 13, 14 da kuma 17.
Mujallar Daily post, ta wallafa cewa shugaban ya kuma kara da cewa yawancin waanda jami'an nasa suka yi awon gaba da su, ba wannan ne karo na farko da 'yan kungiyar suka taba kama su ba. Yanzu haka dai shugaban ya bayyana cewa za a tura dukkan su kotu domin yi masu shari'a akan kama su da laifin aikata karuwanci da sauran wasu ayyukan da suka sabawa doka.