Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN AMURKA: Trump Da Biden Na Ci Gaba Da Nunawa Juna Yatsa


Yan takarar shugaban kasar Amurka Donald Trump da Joe Biden
Yan takarar shugaban kasar Amurka Donald Trump da Joe Biden

Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa manema labarai a jiya Laraba cewa kuru’un da yake samu a jihohin da ake kira da filin daga sun haura manyan binciken jin ra’ayi dake nuna tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden na kasa shi.

“Adadin kuru’un jin ra’ayi suna da kyau. Amma baka ganin adadin kuru’u na ainihi”, inji Trump a lokacin da yake jawabi a otal dinsa a Las Vegas kafin ya tashi zuwa Arizona domin gudanar da tarukan yakin neman zabe guda biyu.

Kuru’un jin ra’ayi na kasa suna nuni da Biden na gaba da Trump da kashi bakwai ko takwas cikin dari amma adadin na raguwa zuwa rabin ratar a jihohin da ake kwatanta su da filin daga wandanda ake gani zasu samar da kuru’un wakilai masu zaben shugaban kasa da ake kira “Electoral College.”

biden-da-trump-sun-ci-gaba-da-sukar-juna-gabanni-zaben-3

zaben-amurka-tarihin-dan-takarar-jam-iyar-republican-donald-trump

zaben-amurka-tarihin-dan-takarar-shugaban-kasa-na-jam-iyar-democrat-joe-biden

Binciken jin ra’ayoyin jama’a na kasa na nuni da cewa Biden yana gaba da Trump da kashi 7 zuwa 8 cikin dari, sai dai yana gaba da kimanin rabin wannan adadin a jihohin da ake fafatawa da mai yiwuwa su zama wadanda zasu tabbatar da wanda zai lashe zaben wakilan Electoral College.

Trump na cewa, binciken ra’ayoyin jama’a da ke nuna yana baya, bincike ne da ake dannewa, kamar yadda ake boye tallafin yakin neman zabe da ake ba kwamitin zabe na kasa na jam’iyar Democrat.

Dan takarar jam'iyar Democrat Joe Biden yana magana a wani gangamin yakin neman zabe a Detroit, (AP Photo)
Dan takarar jam'iyar Democrat Joe Biden yana magana a wani gangamin yakin neman zabe a Detroit, (AP Photo)

Yayin da ake ci gaba da yakin neman zaben shugaban kasa a Amurka, shugaba Donald Trump yace ya bankado wasu sakwannin email da ba a tantance ba da ake zargi na dan dan takarar Democrat ne Joe Biden, da zummar bada mamaki a watan Oktoba, lamarin da ka iya sauya batun takarar baki daya.

Lauyan Trump Rudy Giuliani ne ya bankado sakwanni da ba a tantancen ba da ake ganin an dauko su ne daga komfutar dan Biden, Hunter Biden, wanda ake biyanshi a matsayin mamban hukumar darektocin kamfanin makamashi na Burisma, mallakar wani dan kasar Ukraine, a lokacin da mahaifinsa ke mataimakin shugaban kasa karkashin mulkin Obama, kana yake kula da dangantakar Amurka da Ukraine.

Shugaba Donald Trump yana magana a wani gangamin yakin neman zabe a Circleville, Ohio. (AP Photo)
Shugaba Donald Trump yana magana a wani gangamin yakin neman zabe a Circleville, Ohio. (AP Photo)

Wani sakon da email da aka aika a shekarar 2014 da ake zargin cewa daga Vadym Pozharskyi mai bada shawarar ga kamfanin Burisma, Pozhaskyi ya godewa Hunter Biden da ya shirya ganawa da mataikan shugaban kasa. Abokan adawan Biden suna ganin wannan a matsayin kwakkwarar hujjar cewa iyalan Biden sun sami kudi daga Burisma domin bude mashi hanyar samun gata daga mataimakin shugaban kasa.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya musunta zaragin aikata rashawa, yana mai cewa babu wata ganawa tsakanin shi da Pozhaskyi kana yana kiran sa ido da kwamitin yakin neman zaben Trump ya yi a kan harkar kasuwancin da dansa ya yi a lokutan baya a matsayin wani yunkurin dauke hankalin jama’a daga muhimman batutuwa da suka shafi zaben.

trump-da-biden-sun-yi-muhawarar-karshe-kafin-zabe

muhawarar-mataimakan-yan-takarar-shugaban-kasar-amurka

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG