Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jihar New York Ta Dauki Wasu Sabbin Matakan Kare Jama’a Daga COVID-19


COVID-19
COVID-19

Yayin da hankalin duniya ya karkata a kan yaki tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, birnin New York a Amurka na daukar matakan kare al’ummarsa daga barazanar da cutar coronavirus ke yi a birnin da ya taba zama tungar annobar COVID-19 duniya.

NEW YORK, USA - Tuni hukumomin birnin na New York suka fara fitar da wasu tsare tsaren fadakarwa.

Kwamishinan Lafiya na Birnin New York Dr. Dave A. Chokshi ya ba da sanarwar sabon tsarin fadakarwar lafiya na Covid 19 wanda zai ankarar da mazauna birnin New York game da barazanar cutar da kuma yadda zasu kawar da ita.

Tsarin fadakarwa mai matsayin launuka hudu na tsanani sosai da rashin tsanani ja, ruwan lemu, ruwan dorawa da kuma kore zai nuna abin da ya kamata 'yan New York su yi don kiyaye kansu da makwabtan su.

Matsayin fadakarwa ja na nufi barazana mai girma sosai, ruwan lemu na da girma amma ba kamar ja ba, ruwan dorawa matsakaicin barazana kana kore na nufin babu barazana, suna kuma nuna yarda cutar ke yaduwa tsaknin al'umma. Da zarar birni ya kai matakin ruwan lemo ko ja, hakan na nufin ayyukan kula da lafiya a birnin na cikin tsananin matsin lamba.

Tun da aka fito da wannan tsarin fadakarwa, birnin New York baya fuskantar wata barazana a cewar sashen kiwon lafiya na birnin.

Idan tsarin fadakarwa a birnin ya fuskanci barazana mai yawa, ma'aikatar lafiya ta birnin New York tace jami'anta za su yi la'akari da dawo da bukatun saka abin rufe fuska a cikin manyan wuraren da ke da hadari da wuraren da ba za a iya nisanta da juna ba. Hakanan za su kuma iya duba batun dawo da bukatar yin allurar rigakafi saboda shiga yawancin wuraren dake rufe.

"Za mu aiwatar da matakan da suka dace a kan lafiyar jama'a don kiyaye birninmu. Za mu karfafa matakan idan bukatar yin hakan ta taso. Ba za mu ji tsoron yin wadannan gyare-gyare da canje-canje ba. COVID yana canzawa. Yana sauya salo, yana kuma rikidewa. Dole ne mu kuma mu bi shi a haka," in ji magajin garin birnin New York Eric Adams.

Wasu mazauna birnin New York sun bayyana jin dadinsu game da matakan da hukumomin birnin ke dauke na sanya ido a kan bullar cutar.

An dai riga an bude birnin New York domin ci gaba da hada hada kamar yanda birnin yake a baya kafin barkewar annobar COVID-19 amma duk da haka hukumomi zasu yi taka tsantsan.

Saurari rahoton Baba Makeri cikin sauti:

Jihar New York A Amurka Ta Dauki Wasu Sabbin Matakan Kare Jama’a Daga COVID-19
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

XS
SM
MD
LG