Kungiyar ba da agaji ta yara ta sanar ne a cikin wata sanarwa cewa an cimma yarjejeniyar tare da J & J da ke kasar Belgium.
Za a iya kai karin wasu allurai miliyan 35 na allurar rigakafin zuwa kasashen kungiyar Tarayyar Afirka mai mambobi 55 a karshen wannan shekarar kuma za a iya yin odar wasu allurai miliyan 180 a karshen shekara, in ji UNICEF.
“Dole ne kasashen Afirka su sami wadataccen hanyar samun allurar rigakafin COVID-19 cikin gaggawa. An samu rashin adalci wajen samar da rigakafin, tare da kasa da kashi 1 cikin 100 na yawan mutanen nahiyar Afirka a halin yanzu da suka samu yin allurar rigakafin COVID-19.
Wannan ba zai ci gaba ba a haka, ”in ji Babban Daraktan UNICEF Henrietta Fore. "UNICEF, tare da dadadden tarihin ta na isar da alluran rigakafin a duk duniya, tana tallafawa kokarin allurar rigakafin COVID-19 na duniya ta hanyar AVAT, COVAX, da sauran hanyoyin don kara wadata da kuma samun alluran."
Allurar rigakafin ta J&J ta sami amincewar gaggawa daga Hukumar Lafiya ta Duniya a watan Maris.