A yammacin Jumma'a wasu da ake kyautata cewa 'yan Boko Haram ne sun kai hare-hare garin Damboa inda suka yiwa wani karamin barikin soja da ofishin 'yan sandan garin kurmus da wuta.
Bayan nan su ka kashe sojoji goma sha biyu har da shugaban su, da kuma 'yan sanda biyar da suka hada da wani babban jami'un su wato D.P.O.
Shaidun gani da ido sun tabbatarwa Muryar Amurka cewa mahara masu yawan gaske ne suka yi dirar mikiya a garin, su na sanye da kayan soja, kuma tun da misalin karfe biyar na yammacin Jumma'a suka fara ruwan wuta da kone-kone a garin har zuwa karfe biyun dare sannan suka kama gaban su.
Daga bisani jam'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan jahar Borno D.S.P Gideon Jibrin ya tabbatar da faruwar al'amarin, amma bai yi wani karin haske ba.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka a jahohin Borno da Yobe, Haruna Dauda Biu ne ya aiko da rahoton.