Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Matafiya 6 A Zamfara


Yan bindiga
Yan bindiga

Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan da kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ya yi barazanar kaddamar da hare-hare a kan al'ummomin jihar Zamfara da Sokoto a sabuwar shekarar 2025.

An sace akalla matafiya 6 yayin da 'yan bindiga suka farwa matafiya a kan hanyar zuwa Shinkafi kusa da kauyen Kwanar Jalaf dake karamar hukumar Shinkafin jihar Zamfara.

Al'amarin ya faru ne da safiyar jiya Talata lokacin da maharan suka yi garkuwa da fasinjoji 6 da ke balaguro cikin wata karamar mota kirar Golf tare da cinna mata wuta, abin da ya kara jefa fargaba a zukatan mazauna yankin dama matafiya.

Harin na zuwa ne kasa da mako guda bayan da kasurgumin dan bindigar nan Bello Turji ya yi barazanar kaddamar da hare-hare a kan al'ummomin garuruwan Shinkafin da Zurmi a jihar Zamfara, da kuma na Isah da wasu yankunan jihar Sokoto a sabuwar shekarar 2025.

Mazauna yankin sun shaidawa tashar talabijin ta Channels cewa 'yan bindigar sun datse hanyar, tare da tilastawa motar tsayawa gabanin su sace mutanen dake cikinta sannan suka cinna mata wuta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG