Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan gudun Hijira Na Cikin Tsaka Mai Wuya A Jihar Zamfara


Wadansu ‘Yan Gudun Hijira
Wadansu ‘Yan Gudun Hijira

Fiye da mutane dubu dari (100,000) ne suka rasa matsugunansu saboda tashe-tashen hankula da ake ci gaba da yi a jihar Zamfara, inda da yawa daga cikin su ke fuskantar mawuyacin hali kamar rashin abinci, kiwon lafiya, da matsuguni.

Lamarin dai na da nasaba da cin zarafin bil’adama da ake yi, musamman ga mata da kananan yara, yayin da al’amuran kalubalen tsaro ke kara ta’azzara a jihar.

A yayin bukin ranar tunawa da 'yancin bil’adama, kungiyoyin fararen hula da kungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana damuwarsu kan yadda ake ci gaba da take hakkokin bil'adama a jihar Zamfara. Sun bayyana irin mawuyacin halin da ‘yan gudun hijirar ke ciki, ciki har da rahotannin fyade da sauran nau’ikan tashe-tashen hankula.

Yara 'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa
Yara 'Yan Gudun Hijira A Kauyen Luvu da ke Karu A Jihar Nasarawa

Wadannan kungiyoyi sun jaddada cewa rashin tsaro ya zama babban shinge na farko da ke kawo cikas ga sha’anin ci gaba a Zamfara, wanda ke kara ta'azzara talauci da take hakkin bil'adama.

Ahmad Hashim, shine jami'an Kula da shirye shirye na waya Kungiyar Kula da yan gudun hijira, yace “ana take hakkin yan gudun hijira ta hanyar hana su samun Abinci da muhalli da kiwon lafiya da dai Sauran su.”

Ita kuwa Zaunab Nuhu ta kungiyar Kare hakkin mata cewa tayi “rashin tsaro a jihar na cigaba da jefa yan gudun hijira cikin mawuyacin hali musamman na cin zarafi da muzguna masu a wannan gari.”

Yan gudun hijira
Yan gudun hijira

An jaddada batutuwan da suka fi daukar hankali a jihar a yayin bikin ranar kare hakkin bil'adama ta duniya, inda masu fafutuka da masu aikin jinkai suka yi kira da a dauki matakin gaggawa don magance tauye hakkin bil'adama da ke kara ta'azzara a yankin. Da yawa sun yi nuni da cewa rashin samun sansanonin ‘yan gudun hijira a jihar ya sa ‘yan gudun hijirar fuskantar matsaloli.

A nashi haujin, Shugaban hukumar Kare hakkin biladama ta Kasa reshen jihar Zamfara, Abdullahi Abubakar yace akwai bukatar masu Ruwa da tsaki su tashi tsaye don magance matsalar.

“Abun kullum kara yawa yakeyi, muna yawan samun korafe korafe akan take hakkin biladama, gaskiya ya dace gwamnati ta dauki wani mataki.”

YAN GUDUN HIJIRA
YAN GUDUN HIJIRA

A wani yunkuri na rage radadin talauci da rashin tsaro ke haifarwa, gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya kaddamar da shirin mika kudi a kwanakin baya. Shirin da ke da nufin bayar da tallafin kudi ga al’ummomi masu rauni, wanda mutane dubu arba’in da hudu (44,000) da suka hada da matasa, da masu bukatu na musamman, da kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa za su amfana da tallafin. Ana kallon shirin a matsayin wani kyakkyawan mataki na dakile kalubalen tattalin arziki da kalubalen tsaro ya haddasa a Jihar.

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya shaidawa Sashen Hausa na Muryar Amurka cewa, kalubalen tsaron da jihar fama da shi yayi sauki kuma suna nan suna aiki tukuru don ganin an samu kwanciyar hankali.

Yan gudun hijira
Yan gudun hijira

“Idan na ce ma babu yan gudun hijira banyi adalchi ba, amma mun samarda wani kwamiti da zai yi aikin tantance su don gano yawan su dakuma yadda za mu taimake su da Abinci da Magani da muhalli da dai sauran su “ Inji Gwamna Dauda Lawal

Duk da haka, ma'aikatan jinkai sun lura cewa, duk da cewa irin wadannan shirye-shiryen suna da mahimmanci, ba su isa su magance cikakken yanayin rikicin ba. Yawancin mutanen da suka rasa matsugunansu na ci gaba da fama da yanayin rayuwa na tashe-tashen hankula da kauracewa gidajensu, tare da takaitaccen damar samun ababen more rayuwa da tsaro.

Saurari cikakken rahoton Abdulraz Bello Kaura:

'Yan gudun Hijira Na Cikin Tsaka Mai Wuya A Jihar Zamfara
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:31 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG