Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Saki Alkalin Babbar Kotun Borno Da Aka Yi Garkuwa Da Shi 


Sai dai har yanzu ana cigaba da yin garkuwa da matarsa, Alkalin Majistare Binta Mshelia da direba da dogarinsa jami’in dan sanda.

Mutanen da suka yi garkuwa da alkalin babbar kotun jihar Borno, Mai Shari’a Haruna Mshelia sun sake shi.

Sai dai har yanzu ana cigaba da yin garkuwa da matarsa, Alkalin Majistare Binta Mshelia da direba da dogarinsa jami’in dan sanda.

Wata majiya mai tushe ce ta tabbatar da sakin alkalin.

An ruwaito majiyar na cewa, “godiya ta tabbata ga Allah! yanzu muka samu labarin sakin Mai Shari’a Haruna Mshelia daga hannun Boko Haram. Muna rokon Allah ya kare mu daga kowane irin ibtila’i.”

Idan ba’a manta ba, a ranar Litinin 24 ga watan Yunin daya gabata ne, wasu ‘yan bindiga suka sace Mai Shari’a Mshelia da matarsa da direba da dan sanda dake musu rakiya.

A cewar majiyoyin dake kusa da iyalin, Mai Shari’a na yin balaguro ne daga birnin Biu zuwa Maiduguri tare da matarsa, ita ma babbar ma’aikaciyar shari’a, lokacin da wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG