Rahotanni daga jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya na cewa Sarkin Gobir na garin Gatawa Alhaji Isa Muhammad Bawa ya rasu a hannun ‘yan bindigar da suka sace shi.
Kwanaki 25 da suka gabata aka yi garkuwa da Sarki Bawa da dansa da wani dan uwansa.
Babu dai cikakkun bayanai kan abin da ya yi sanadin mutuwarsa.
Wasu sassan jihar Sokoto na daga cikin yankunan da ‘yan bindiga suka mamaye a arewa maso yammacin Najeriya inda suke kai hare-hare a duk lokacin da suka bushi iska.
Tuni har tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya mika sakon ta’aziyya ga iyalai da al’umar masarautar ta Gobir.
“Ina mai mika ta’aziyya ga iyalai da daukacin al’umar Gobir da gwamnatin jihar Sokoto dangane da wannan rashi na Sarkin Gobir, Alhaji Isa Bawa.” In ji Atiku.
“Irin wannan danyen aiki da ‘yan bindiga ke yi wanda har ya kai ga rasuwar wannan fitaccen shugaba, wani abu ne da ke mana tuni kan bukatar a tsaurara matakan tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a.” Atiku ya kara da cewa.
Ya kara da cewa, “ya zama wajibi mu nanata cewa dole ne gwammati ta tabbatar da tsaro da zai kare rayukan jama’a, saboda kada mutane su rika rayuwa cikin fargabar fadawa hannun ‘yan bindigar.”
Dandalin Mu Tattauna