Lamarin ya auku ne a daren ranar Lahadi, inda shaidun gani da ido suka ce mahara kusan 20 dauke da muggan makamai sun kai farmaki a gidan kwamishinan watsa labaran jihar ta Naija, Mohammed Sani Idris da ke Baban Tunga a cikin karamar hukumar mulkin Tafa.
Mazauna yankin sun ce sun ji karar harbe-harbe sosai da ‘yan bindigar suka yi a iska, kafin kutsawa cikin gidan kwamishinan.
Nan take dai suka sami kwamishinan, suka kuma yi awon gaba da shi, amma basu tafi da matarsa ba da take tare da shi a lokacin.
Gwamnatin jihar ta Naija dai ta tabbatar da aukuwar lamarin, a wata sanarwa da kakakin gwamnatin jihar, Marry Noel-Berje ta fitar.
Sanarwar ta ce da misalign karfe 1 na safiyar Litinin ne maharan suka sace kwamishinan a gidansa na Baban Tunga.
Ta kara da cewa jami’an tsaro na nan suna bi-biyar da ‘yan bindigar domin kama su da kuma kubutar da kwamishinan.
Wannan al’amari na zuwa ne kwana daya bayan da wasu ‘yan bindigar suka kai wani harin a kauyukan Karen Bana da Bobi, inda suka hallaka akalla mutane biyu, suka kuma yi awon gaba da wasu, ciki har da shugaban jam’iyyar APC na yankin arewacin jihar ta Naija, Alhaji Aminu Bobi, a yayin da yake a gonarsa.