A daren ranar Alhamis ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da shugaban jam’iyyar PDP na jihar Legas, Philip Aivoji, a hanyar Legas zuwa Ibadan, a lokacin da yake dawowa daga taron jam’iyyar na shiyyar Kudu-maso-Yamma a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.
Dan takarar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023, Dr. Abdul-Azeez Adediran, ya bayyana kaduwarsa da labarin sace shugaban jam'iyyar a kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.
Adediran ya bayyana lamarin a matsayin wani abu mai daure kai ga karuwar rashin tsaro a Najeriya musamman a yankin Kudu maso Yamma.
Ya dora alhakin hakan kan gazawar gwamnati a fannin tsaro, duk da cewa hakan ya jefa rayuwar ‘yan kasa cikin hadari, don haka ya bukaci daukar matakin gaggawa daga jami’an tsaro domin a gaggauta sakin shugaban jam’iyyar da aka sace.
Ya kuma shawarci jami’an tsaro na yankin, Amotekun su hada kai da ‘yan sanda a wannan aikin ceto.
A gefe guda kuma rahotanni daga Najeriyar na cewa rundunar jihar Oyo ta ce tan kan bibiyar mutanen da suka yi garkuwa da shugaban jam'iyyar ta PDP a cewar jaridar Daily Trust.
Dandalin Mu Tattauna