Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 7, Sun Yi Garkuwa Da Fiye Da 70


Jana'izar wa 'yanda 'yan bindiga suka kashe.
Jana'izar wa 'yanda 'yan bindiga suka kashe.

A yayin da ake ganin hare-haren 'yan-bindiga sun yi sauki a watan Ramadan, al'umar garuruwan Kuriga da Udawa da kewaye dake karamar hukumar Chukun jahar Kaduna sun ce su hare-haren ma ta'azzara su ka yi a wannan wata na Azumi. 

Daya daga cikin al'umar yankin, Malam Yusuf Ibrahim Udawa ya ce 'yan-bindigan sun hallaka mutane da dama kuma su na rike da mutane sama da saba'in su na jiran kudin fansa.

Duk da jingina hauhawar hare-haren 'yan-bindiga da wasu ke yi kan dagewar da gwamnatin Kaduna ta yi cewa ba sulhu da 'yan-bindiga, gwamna Nasiru Ahmed El-rufa'i ya ce ya nan kan wannan matsaya don ita ce za ta magance matsalar satar mutane don neman kudin fansa.

Jahar Kaduna dai na cikin jahohin Arewa maso yamman da ke fama da hare-haren yan-bindiga sai dai matsalar ta dan yi sauki a baya kafin sake fillar maharan dajin da kan hana al'uma sukuni da sakewa.

Saurare cikakken rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG