Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

El-Rufai Ya Dade Bai Kama Mu Ba - Iyayen Daliban Da Aka Sace


Iyayen Daliban da aka sace a Kaduna suna zanga-zanga.
Iyayen Daliban da aka sace a Kaduna suna zanga-zanga.

Iyayen daliban kwalejin koyon fasahar aikin gona da gandun daji ta tarayya ta Kaduna da aka sace, sun yanke shawarar sasantawa da ma biyan kudin fansa domin ceto ‘ya’yansu da yanzu haka suke hannun ‘yan bindiga.

A wani taron manema labarai da suka gudanar a harabar kwalejin ta koyon fasahar aikin gona da gandun daji ta tarayya, iyayen yaran sun ce sun yanke kauna akan kokarin da gwamnati ke cewa tana yi domin ganin an sako ‘ya’yan nasu.

Akan haka suka yanke shawarar bin hanyar tattarawa da biyan kudin fansar yaran na su, ko da kuwa gwamnan jihar ta Kaduna Nasir El-Rufai zai sa a kama su.

Gwamnatin jihar dai ta yi barazanar kamawa tare da hukunta duk wanda aka samu yana sasantawa da ‘yan ta’adda a jihar.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

To sai dai iyayen sun ce sun gaji da zama a cikin ukuba da bakin ciki, don haka ba sa tsoron duk wata barazana ta gwamnati, na kama su da laifin sasantawa da ‘yan bindiga domin ceto rayuwar ‘ya’yansu.

Karin bayani akan: ​Nasir El-Rufai, 'Yan bindiga​, Kaduna, Nigeria, da Najeriya

Tuni kuma da iyayen yaran suka soma tuntubar wasu kungiyoyi masu zaman kan su da hukumomin ba da tallafi, domin su taimaka wajen ganin an sako yaran.

Mai Magana da yawun iyayen Comrade Friday Sani, ya ce sun cire tsammani daga samun taimakon gwamnati wajen tabbatar da an sako yaran, tun sa’adda gwamnatin jihar ta fitar da sanarwar cewa gwamna Nasir El-Rufai ya ce ba zai “biya kudin fansa ga ‘yan ta’adda ba, ko da kuwa dan sa ne aka sace.”

Rescued Abducted Kaduna school Children.
Rescued Abducted Kaduna school Children.

Ya ce ‘yan bindigar sun kira iyayen yaran daya bayan daya, suka nemi a biya kudin fansa, suka kuma yi barazanar idan ba’a biya ba, za su aure ‘yan matan, su kuma karkashe mazajen, lamarin da sani ya ce iyayen ba za su iya jurewa haka kawai ba tare da daukar wani mataki ba, ko da kuwa gwamnati za ta kama su.

“Babban abin takaici ma shi ne, tun sa’adda wannan lamari ya auku, har kawo yanzu gwamnatin tarayya ba ta fitar da wata sanarwa akan wani yunkuri da take yi na ceto yaran ba,” in ji Comrade Sani.

Ya ci gaba da cewa “gara gwamnati ta kama mu, da mu ci gaba da kasancewa a cikin wannan mawuyacin halin da gwamnatin ta saka mu. Don haka gwamnati ta sani ba ma tsoron kamun ta, domin idan muna tsare a hannun hukuma, ya fi a ce yaran mu ba sa a gida.”

Kalejin Fasahar Aikin Gona Da Gandun Daji ta Tarayya Da Ke Kaduna
Kalejin Fasahar Aikin Gona Da Gandun Daji ta Tarayya Da Ke Kaduna

To sai dai kuma a martanin da ta mayar, gwamnatin jihar ta ce ba’a fahimci umarnin na gwamnati ba, domin kuwa ba inda ya shafi iyayen da aka sace ‘ya’ya ko ‘yan uwansu.

A cikin wata sanarwa, kwamishinan tsaro da lamurran cikin gida Samuel Aruwan, ya ce gargadin na kamawa da hukuntawa ya shafi wadanda ke ayyana kan su a matsayin wakilan gwamnati domin sasantawa da ‘yan bindiga, saboda biyan wasu bukatu na kashin kan su, amma ba iyaye ko ‘yan uwan daliban da aka sace ba.

Aruwan ya ce wannan “bata suna” da ake wa gwamnati kuma, ba zai hana ta ci gaba da yin aiki tukuru ba, domin tabbatar da yaki da ayukan ‘yan ta da kayar baya a jihar.

“A karshe ba za mu shiga sa-in-sa da iyayen yaran ba, domin muna sane da irin halin da suke ciki, mu ke kuma alhini tare da su, tare da manufa daya ta tabbatar da an sako dukkan daliban da aka sace,” in Samuel Aruwan.

Tun a ranar 11 ga watan Maris ne dai ‘yan bindiga suka kai farmaki a kwalejin ta koyon fasahar aikin gona da gandun daji, inda suka yi awon gaba da dalibai 39.

Gwamnan Kaduna a yayin karbar mutanen da sojoji suka kubutar daga hannun 'yan bindiga.
Gwamnan Kaduna a yayin karbar mutanen da sojoji suka kubutar daga hannun 'yan bindiga.

An sako dalibai 10 daga cikinsu, a yayin da har yanzu dalibai 29 na hannun ‘yan bindigar.

A ‘yan kwanakin baya ne kuma 'yan bindigar​ suka saki wani hoton bidiyo da ya karade Kafofin sada zumunta, da ke nuna yaran da aka sace a cikin jeji, ana dukan su suna kuka da neman agajin biyan bukatun ‘yan bindigar domin a sako su.

‘yan bindigar na neman a biya su naira miliyan 500, kudin fansar sauran daliban 29 da ke hannunsu.

Daliban Kaduna da sace
Daliban Kaduna da sace

Ayukan 'yan bindiga da suka hada da kai farmaki, kisan jama'a da satar mutane domin karbar kudin fansa na kara yawaita a jihar ta Kaduna a 'yan makwannin baya-bayan nan, lamarin da masu fashin baki musamman a kan sha'anin tsaro, suke alakantawa da furucin gwamnan jihar Nasir El-Rufai, na cewa ba zai taba yin sulhu da 'yan ta da kayar baya ba.

XS
SM
MD
LG