Lamarin ya auku ne da safiyar yau Litinin, inda ‘yan bindigar suka sami nasarar kona wasu ofisoshi da kuma motoci a shelkwatar ‘yan sandan.
Har kawo yanzu ba’a kai ga gano musabbabi, ko wadanda ke da alhakin kai farmakin ba.
Wata majiya ma fi kusa da ‘yan sanda, ta tabbatar da cewa jami’an ‘yan sandan da ke shelkwatar sun yi kokarin hana maharan kai wa ga wajen adana makamai na shelkwatar.
To sai dai majiyar ta kasa bayyana kiyasin barnar da harin ya haifar, da kuma ko ya shafi wasu jami’ai, kasancewar “babu tabbatattun bayanai akan harin” ya zuwa lokacin rubuta wannan labarin.
Wasu shaidun gani da ido sun ce sun ji karar harbin manyan bindigogi kafin cinnawa ofoshin wuta.
Ya zuwa lokacin hada wannan labarin, ba wani bayani daga rundunar ‘yan sandan Najeriya dangane da wannan lamarin.
A wata mai kama da wannan kuma wasu ‘yan bindigar sun kai hari a wani ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar mulkin Bende ta jihar Abia, inda su ma suka cinnawa ofishin wuta.
Lamarin ya auku ne da sanyin safiyar Litinin, to amma majiyoyi da ke makwabtaka da ofishin ‘yan sandan, sun ce maharan na dauke ne da muggan makamai a lokacin farmakin.
Wannan farmakin dai daya ne daga cikin jerin hare-haren da ‘yan bindiga suke kai wa ofisoshin ‘yan sanda a jihar ta Abia da ma makwabtan jihohi a ‘yan kwanan nan, lamarin da ya kai ga kakaba dokar hana fitar dare a garuruwan Aba, Umuahia, Ohafia da Arochukwu.
Ko baya ga dokar ta hana fitar dare, gwamnatin jihar ta kuma ankarar da jama’a cewa, wasu mayaka sun shirya kai jerin hare-hare a wasu sassan jihar, don haka kowa ya lura, tare da yi taka-tsantsan.