Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane Da Dama A Wasu Kauyukan Karamar Hukumar Kanam


Yan bindiga
Yan bindiga

Bayanai daga wassu kauyukan karamar hukumar Kanam a jahar Filato na nuni da cewa mahara sun kashe mutane da dama a kauyukan dake yankin.

Wadansu mazauna yankin da Muryar Amurka ta zanta dasu sun bayyana cewa, ‘yan bindigar dauke da muggan makamai sun shiga kauyukan ne da tsakar ranar jiya Lahadi suka kashe mutane a kauyuka da dama da ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomi basu bayyana adadin su ba.

Ba-saraken kauyen Shuwaka Hudu Ibrahim ya yi Karin haske a kan wannan batu hirar shi da Sashen Hausa ya bayyana cewa, masu garkuwa da mutanen sun shiga Kukawa da kauyukan dake yankin kafin daga bisani suka shiga Shuwaka kuma tuni suka kirga gawarwaki bakwai a Shuwaka.

Ya kara da cewa mutanen sun kona shaguna da gidaje da dama amma a garin Kukawa ba a iya gane adadin mutanen da suka kashe ba kamar yanda aka bayyana musu ta waya a can garin na Kukawa. Kana Ya ce ‘yan banga dake taimaka musu kuma an karkashe su.

Sarkin na Shuwaka ya ce babu wani dauki da suka samu daga jami’an tsaro, kuma tun cikin watan Disamban bara suka yita kira a kawo musu dauki amma babu wanda ya saurari kokensu.

Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya fadawa wakiliyar Sashen Hausa mutane da dama sun tsere daga gidanjensu suna boya a cikin dazuka. Shima ya ce maharan sun shigo kauyukan ne a kan Babura kuma sun kashe mutane fiye da dari.

Shugaban karamar hukumar Kanam, Dayyabu Yusuf Garga ya shaida cewa ya zuwa yanzu an yi jana’izar mutane ishirin da biyar yayinda jami’an tsaro suka bukaci a karo musu dakaru don tinkarar ‘yan bindigar.

Ga dai rahoton Zainab Babaji daga Jos:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG