Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutane 12 Sun Mutu Sanadiyar Malalowar Tabo A Phillipines


A rescue team wades into flood waters to retrieve a body in Tacloban, central Phillipines, Nov. 13, 2013.
A rescue team wades into flood waters to retrieve a body in Tacloban, central Phillipines, Nov. 13, 2013.

Hukumomin Kasar Phillipines sun ce, mutane 12 sun mutane, kusan 50 sun bace kuma ana fargabar sun makale a baruguzan gine-ginen sakamakon binne gidaje da kwararowar laka ta yi

Akalla mutane 12 sun mutu bayan da wata gagarumar zaftarewar laka ta binne gidaje da yawa a tsakiyar kasar Philippines yau Alhamis.


Bala’in na baya-baya nan ya faru ne sa’o’i bayan fitowar rana a birnin Naga dake tsibirin Cebu. Kwana da kwanakin da aka kwashe ana tapka ruwan sama kamar da bakin kwarya shi ya zaizaye lakar a kan tsaunuka, abinda ya bankado laka da duwatsu kan wasu gidaje.

Hukumomin yankin sun ce mutane kusan 50 sun bace kuma ana fargabar sun makale a baruguzan gine-ginen.


Lamarin da ya faru yau Alhamis na zuwa ne a yayinda mazauna tsibirin Luzon ke kokarin farfadowa daga bala’in zaftarewar laka da suka faru a yankin sakamakon mahaukaciyar guguwar teku Mangkhut.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG