Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 17 a Jihar Gwambe


Ma'aikatan Agajin Gaggawa na Red Cross.
Ma'aikatan Agajin Gaggawa na Red Cross.

Hukumar bada agajin gaggawa wato Red cross a jihar Gombe tabada lissafin yawan mutanen da wasu ‘yan bindiga suka kashe a matsayin goma sha bakwai da suka hada da farar hula dakuma masusa kayan sarki.

Kashe mutanen dai yafarune agaruruwan Nafada da kuma karamar hukumar funakaye a jihar Gwambe a ranar talatar data wuce. Abubakar Yakubu Gwambe shine sakataren kungiyar agajin gaggawa ta kasa da kasa bangaren jihar Gwambe, ya tabbatar wa da wakilin Muryar Amurka cewa an kashe masu fararen hula mutum biyar, dakuma dan sanda guda daya, sai kuma soja guda biyar. A Ashaka kuma tsakanin karamar hukumar Funakaye an kasahe mutum shida, gaba daya dai jimlar mutanen da aka kashe sun kai goma sha bakwai.

Kungiyar bada agajin gaggawa ta red cross na cigaba da bada taimako ga masu bukatar kulawa ta gaggawa. Jihar Gwambe dai ta fuskanci hare haren ‘yan bidiga gami da tada boma bomai a cikin wannan lokuta.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:25 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG