Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumar INEC ta Dage Aikin Raba Katin Rajistar Zabe


Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Professor Attahiru Jega.
Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, (INEC) Professor Attahiru Jega.

A jahohin Naija da Katsina da Kaduna da kuma Borno.

Hukumar zaben Najeriya mai zaman kan ta, INEC a takaice, ta bada sanarwar dage aikin raba katin rajistar zaben da ta shirya farawa Jumma'ar nan a jahohin Naija da Katsina da Kaduna da kuma Borno.

Yanzu dai hukumar zaben ta INEC ta ce sai ranar 28 ga watan nan na Nuwamba za ta fara wannan aiki.

Domin jin dalilai ko matsalolin da suka sa Hukumar zaben daukan wannan mataki na canza lokacin fara raba katin rajistar zaben a jahohin Naija da Katsina da Kaduna da kuma Borno wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya tuntubi kakakin hukumar zaben Mr.Nick Dazang wanda yayi karin haske kamar haka:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye

Duk da bayanin da hukumar INEC ta yi, 'yan jam'iyyar APC ta adawa a kasar Najeriya na ganin cewa akwai wata boyayyar manufa kuma akwai wani shirin neman kuntata mu su.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG