Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabanni a Jihar Adamawa na Kwashe Iyalansu Suna Guduwa


Jihar Adamawa.
Jihar Adamawa.

Yanzu haka dai tuni talakawa a jihar Adamawa sun fara kokawa da abun da suka kira halin ko-in-kulan da suke zargin shugabannin jihar ke nunawa na cigaba da kwashe iyalansu suna ficewa daga jihar.

Kamar dai yadda bayanai ke nunawa wasu kusoshin gwamnati da manyan ‘yan siyasar jihar da ma sarakuna iyayen al’umma tuni suka kwashe iyalansu suka fice, biyo bayan kwace garin Mubi da yan kungiyar Boko Haram suka yi, yau fiye da mako guda kenan.

Jama’a dai na kokawa kan ficewar da manyan jihar keyi, ata bakin wasu ‘yan Adamawar sun bayyana wannan lamari kan cewa abin takaicine kasancewar a wannan lokaci da su manyan yakamata ace suna zuwa suna taimakawa talakawa wanda suka shiga cikin mugun matsayi, amma sai dai aji cewar sune ma ke kama hanya suna gudu. Shi kuma Mohammed wani dan Adamawar yace, “basu kyautawa talakan kasarnanba saboda idan akace maka shugaba yabar gari to ina talaka zaije,”

Duk da wannan hali shi kuwa sarkin Mubi Alhaji Abubakar Isa Ahmadu yayi yinkurin komawa garin, duk dama garin tuni yana hannun ‘yan Boko Haram dama tuni suka sauyawa garin suna ya koma Madinatul Islam, kuma an dai hana shi komawa garin. Saurari cikakken rahoton Ibrahim Abdul’Aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG