Da yake magana kan wannan batu shugaban kungiyar matasan da ake kira kato da Gora, ko civilian JTF kwamanda Ali Gwani, yace kuskure ne jama'a su nade hanu su zaci cewa akwai wadanda zasu kare su, tilas kowa ya zama jami'in tsaro.
Jama'a da suke gudun hijira sun bayyana irin bakar wahala da suka shiga, kamin su kai ga inda suke yau. Wani wanda yayi magana da wakilin Sashen Hausa a Yola yace da wani mai tabin hankali suka yi gudun tsira.
Dubbaan jama'a ne suke ci gaba da yin gudun hijira daga Mubi birni na biyu a girma a jihar Adamawa zuwa fadar jihar da kuma wasu sassan Najeriya daban daban.
Ga karin bayani.