Kasurgumin dan bindigar nan Dogo Gide ya bukaci wasu garuruwa 23 da ke shiyar Tsafe ta Yamma karkashin karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara su biya harajin fiye da Naira miliyan 100.
An bukaci kowane daga cikin garuruwan su biya wani kayadajjen adadi na kudi, inda aka dorawa garuruwan Kunchin Kalgo (Naira miliyan 20), Sungawa (Naira miliyan 15) da Rakyabu (Naira miliyan 15) adadi mafi yawa.
Harajin da shugaban ‘yan bindigar da ake nema ruwa a jallo ya kakaba ya haddasa zaman dar-dar a yankin inda mazaunansa ke fafutukar sauke wannan nauyi saboda fargaba harin ramuwar gayya.
A hirarsa da tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho, kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara Muhammad Dalijan, ya tabbatar da hakan sai dai ya ba da tabbacin cewa suna sanya idanu a kan lamarin.
Ya kara da cewa an tura jami’an tsaro zuwa garuruwan da al’amarin ya shafa domin dakile kai hare-hare da tabbatar da doka da oda.
“Gaskiya ne!, kasurgumin dan bindiga Dogo Gide ya kakabawa wasu garuruwa haraji, sai dai mun tura jami’anmu zuwa wuraren, babu wanda zai musu barazana, akwai jami’an tsaro a garuruwan.”
“Babu wani gari da ya zama kufayi, babu wanda ya bar gidansa saboda barazanar,” a cewar Dalijan.
Saurari rahoton Abdulrazak Bello Kaura:
Dandalin Mu Tattauna