‘Yan bindiga sun yi garkuwa da limaman majami’ar “Church of Brethren in Nigeria” da aka fi sani da Ekklesiyar Yan’uwa a Najeriya (EYN).
Limaman da al’amarin ya rutsa dasu sun hada da babban limamin EYN na garin Mbila-Malibu da ke karamar hukumar Song, Rabaran James Kwaywng da sakatarensa, Rabaran Ishaku Chiwar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar adamawa, Suleiman Nguroje, ya bayyana a ya Litinin cewar an sace mutanen ne a daren jiya Lahadi, 29 ga watan Disamban da muke ban kwana da shi.
Babban jagoran majami’ar ta EYN, Rabaran Daniel Mbaya, wanda shima ya tabbatar da yin garkuwa da mutanen, ya bukaci jami’an tasaro dasu gaggauta daukar matakan tabbatar da an kubutar da limaman cocin cikin lumana.
Ya kuma bukaci mambobin cocin na EYN da sauran ‘yan Najeriya su taimaka da addu’o’in samun kubutar mutanen.
Dandalin Mu Tattauna