A Jihar Zamfara al'ummomin Kauyukan Adabka da Mallawa sun gwabza fada da ‘yan bindiga har suka samu nasarar kwato wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, duk da cewa an samu hasarar rayuka a kowane bangare.
A yayin wani gumurzu da aka yi tsakanin Jami'an tsaron hadin gwiwa da al'ummomin Kauyukan Adabka da Mallawa da wasu makwaftansu a Karamar Hukumar Bukkuyum ta Jihar Zamfara, an kwato wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, an kuma samu mutuwar mutane daga bangarorin biyu.
Dauki ba dadin da aka yi dai ya biyo bayan tare Hanya tsakanin Adabka zuwa Mallamawa da ‘yan bindiga su ka yi har su ka yi garkuwa da wasu matafiya, lamarin da ya harzuka jami’an tsaro, da askarawa hadi da ‘yan sakai su ka yi artabu da ‘yan bindigar. Kamar yadda Bilyaminu Barau, daya daga cikin wadanda su ka yi fadan, ya ce, daga cikin wadanda aka kashe har da jami'in dan sanda.
“Jiya sun zo tun da safe suka dauki mutanenmu; mu kuma muka tare su a wani kauye da ake ce ma Yar-Gusau. Nan mu ka yi harbe-harbe har suka kashe mana mutun hudu.” Inji Bilya. Haka ma ya ce ‘yan bindigar sun tafi masu da wasu mutane da suka hada da mata da maza, wanda yanzu haka suna hannun su.
Shi ma wani daya daga cikin wadanda suka kubuto daga hannun ‘yan bindigar a yayin fafatawar ya bayyana yadda lamarin ya wakana.
Da yake bada tabbacin faruwar lamarin. Dan Majalisar Tarayya Mai wakiltar mazabun Bukkuyum da Gummi a Majalisar Wakilai ta Tarayya, Engr Suleiman Abubakar Mahmud Gummi, ya ce jami’an tsaro da askarawan Zamfara da ‘yan sakai sun yi kokari matuka wajen hana ‘yan bindigar tafiya da mutanen da su ka yi garkuwa da su.
“Yan bindigar sun kashe Mopol daya da wani dan sakai da wasu mutane biyu kuma sun tafi da wasu,” inji Danmajalisa Engr Suleiman.
Ya ce suna kan daukar matakai don ganin an kara wa jami’an tsaro kayan aiki a yankin musamman wajen gabatar da koke a zauren majalisar wakilai don ganin an dauki matakin samar da isassun kayan aiki ga jami’an tsaro.
Tuni dai gwamnatin Jihar Zamfara a ta bakin Mai bai wa gwamnan shawara kan kafafen yada Labarai, Mustapha Jafaru Kaura, ta bai wa al’umar Jihar damar kare kansu a duk lokacin da ‘yan bindigar suka kai masu hari.
Saurari cikakken rahoton Abdulrazak Bello Kaura:
Dandalin Mu Tattauna