A hira da wakilin Sashen Hausa na Muriyar a Amurka a yankin, kwamishina Gwari yace saboda haka ne ma ya bada lambar woyarsa ga duk wanda yake da bayani da yake so ya baiwa hukumar ba tareda ya bayyana kansa ba. Mallam Akila yace mutane sun san wadanda suke tareda su saboda haka wajibi ne su bada gudumawarsu wajen ganin an inganta harkokin tsaro.
Da ya nemi jin ta bakin wasu daga cikin jama'ar jihar kan wannan kira da kwamishina Akila yayi, wakilin Sashen Hausa lamido Abubakar Sokoto yace wadanda ya zanta da su sun bayyana amincewarsu da tareda alkawarin bata hadin kai ga rundunar.