Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane 3 Tare Da Sace Manoma 2 A Neja


Yan bindiga
Yan bindiga

Shugaban Karamar Hukumar Mariga, Abbas Musa Kasuwa-Garba, ya tabbatar da afkuwar harin tare da jajantawa iyalan wadanda al’amarin ya rutsa dasu.

Harin da ‘yan bindiga suka kai a Lahadin data gabata, ya hallaka mutane 3 sannan an sace wasu manoman shinkafa 2 a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Harin ya afku ne da misalin karfe 9 na safiya tsakanin garin Bangi da Kotonkoro.

Maharan da aka yi ittifakin ‘yan bindiga ne, sun datse hanyar, tare da bude wuta a kan ababen hawan dake bin hanyar.

A cikin wadanda al’amarin ya rutsa dasu akwai direban wata karamar mota da wata karamar yarinya da kuma wani fasinja da aka bayyana sunansa da Alhaji Ibrahim.

Rahotanni sun bayyana cewar mutanen na kan hanyarsu ta zuwa kasuwa ne lokacin da harin ya afku.

Mamallakin motar, Shehu Kotonkoro, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya bayyana damuwa game da matsalar rashin tsaro a yankin. Ya kara da cewar, harin ya faru ne kilomita 5 daga garin Kotonkoro.

Baya ga kisan, an kuma sace wasu manoman shinkafa 2 dake aikin girbi a gonarsu mai nisan kimanin kilomita 2 daga garin.

Shugaban karamar hukumar Mariga, Abbas Musa Kasuwa-Garba, ya tabbatar da afkuwar harin tare da jajantawa iyalan wadanda al’amarin ya rutsa dasu.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG