Al’ummar Nibo dake karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra sun afka cikin rikici a jiya lahadi bayan da ake fargabar cewar ‘yan bindiga sun hallaka mutanen da ba’a san adadinsu ba a kusa da kasuwar Oye Nwochichi dake daura da asibitin karbar haihuwa na garin.
A cewar shaidun gani da ido, batagarin sun zo ne a cikin mota kirar jif “Lexus” mai launi ruwan kasa kuma ba tare da bata lokaci ba suka budewa mutane wuta.
Duk da cewar ba a kai ga tantance yawan mutanen da suka harbe din ba, al’ummar garin sun ce zuwa yanzu an gano akalla gawawwakin mutane 10.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da harin yace al’amarin baya rasa nasaba da fadan kungiyoyin matsafan dake gaba da juna.
Ikenga ya kara da cewar kwamishinan ‘yan sandan jihar, Nnaghe Itam, ya ba da umarnin tura karin jami’an ‘yan sanda zuwa yankin sannan ya bukaci mutanen da suka shaida afkuwar lamarin dasu taimaka da bayanai domin daukar matakin da ya dace.
“Rundunarmu na sane da abinda take zarki rikicin kungiyoyin matsafan da basa ga maciji da juna ne a yau 20/10/2024 a garin Nibo dake karamar hukumar Awka ta Kudu kuma kwamishinan ‘yan sanda, CP Nnaghe Obono Itam ya ba da umarni a gaggauta tura karin jami’an ‘yan sanda zuwa yankin domin daukar matakin da ya dace.
Dandalin Mu Tattauna