‘Yan bindigar daji sun kai wani hari a garin Dayi da ke karamar hukumar mulki ta Malumfashi a jihar Katsina ta arewacin Najeriya, inda suka kashe hakimin garin, tare da yin awon gaba da iyalansa da na wani makwabcinsa.
Lamarin ya auku ne da misalin karfe 9 na daren ranar Juma’a, sa’adda ‘yan bindigar suka shiga garin inda kai tsaye suka nufi gidan basaraken mai suna Alhaji Tanimu Garba, suka kuma harbe shi har lahira.
Shugaban karamar hukumar mulki ta Malumfashi, Maharazu Dayi ya tabbatar da kai harin, inda ya ce bayan kashe mai garin, ‘yan bindigar “sun kuma tafi da matansa 2, daya tana da juna biyu yayin da dayar kuma take da goyo.”
Haka kuma a cewarsa, sun shiga gidan wani makwabcin basaraken inda a can ma suka yi awon gaba da matansa biyu, daya tana da goyo, tare kuma da wani matashi.
‘’Bayan samun labarin na yi kokarin kiran jami’an tsaro na soji da ‘yan sanda da ma ‘yan banga, wadanda kuma suka yi gaggawar isa garin, to amma kuma tuni da 'yan bindigar suka arce bayan gama aika-aikar ta su,” in ji shugaban karamar hukumar.
Ya kara da cewa “a daidai wannan lokaci akwai sauran shuke-shuken amfanin gona kamar dawa da masara, wanda ke baiwa ‘yan ta’addar saukin bacewa idan suka kai farmakinsu.”
Maharazu Dayi ya ce duk da ya ke jami’an tsaro har ma da jama’ar garin sun yi kokarin bin sawun ‘yan bindigar domin ceto mutanen da suka sace, to amma kuma haka ba ta cimma ruwa ba.
A kan haka ya ce majalisar karamar hukumar ta gudanar da wani taron gaggawa da jama’ar garin don samo hanyoyin tabbatar da tsaro da magance aukuwar irin wannan hari nan gaba.
Yanzu haka an kama wasu mutane 3 da ake zargin suna da wata masaniya kan harin da aka kai, yayin da jami’an tsaro su ke ci gaba da bincike.
Saurari rahoton Sani Shu’aibu Malumfashi.
Dandalin Mu Tattauna