Ministan tsaron Najeriya Alh. Badaru Abubakar ya ce, makaman da ake samu a hannun 'yan-bindiga na jami'an tsaron Najeriya, sun sace su ne yayin da suke kai hari.
Ministan tsaron Alh. Muhammadu Badaru Abubakar wanda ya kai wa rundunonin sojan Najeriya a Kaduna ziyarar wuni biyu, ya ce ganin yadda sojojin Najeriya suke ta hallaka manyan 'yan-bindiga a arewa maso yamma ne yasa ya kai wannan ziyarar don karfafa musu gwiwa, sannan ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tunibu ya ce ya jinjinawa sojojin a madadin sa bisa irin na mijin kokarin da su ke yi don magance matsalar tsaro a arewa maso yammacin Najeriya.
La'akari da zargin da mai-baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribado ya yiwa jami'an tsaron, ya sabawa kalaman ministan tsaron Najeriya ya sa wasu 'yan-Najeriya yin kira da ya kamata a gudanar da bincike.
A game da batun bukatar sulhu da 'yan-bindiga kuma, Muhammadu Badaru Abubakar ya ce babu yaki da 'yan-bindiga ne burin gwamnati yanzu ba batun sulhu ba.
Batun hare-haren 'yan-bindiga dai na cikin manyan matsalolin tsaron da suka addabi yankin arewa maso yammacin Najeriya, sai dai ana sa ran cewa za a kafa sabuwar cibiyar tsaro da gwamnati ta sanar don hada ayyukan jami'an tsaron yankin baki daya wanda zai iya taimakawa wajen magance matsalar cikin gaggawa.
Dandalin Mu Tattauna