Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Gano Dakarun Soji Dake Da Laifi A Harin Bam Na Tudun Biri


 Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba
Daraktan Yada Labaran Ma'aikatar Tsaron Najeriya, Manjo Janar Edward Buba

Daraktan Yada Labarai na Ma’aikatar Tsaron Najeriya, Edward Buba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a yayin hirar da yayi dasu a shelkwatar tsaron kasar dake birnin Abuja, a yau Alhamis.

Shugabancin Rundunar Sojin Najeriya yace ya kammala binciken da aka jima ana jira game da kai harin bama-bamai akan ‘yan Najeriya da basu san hawa ba, basu san sauka ba a kauyen tudun biri dake karamar hukumar Igabin jihar Kaduna.

Rundunar tace zata gurfanar da dakarunta guda 2 da aka samu da hannu a laifin gaban kotun soji, inda tace tun farko ma bai kamata a kai harin ba.

Rundunar Sojin Najeriya, wacce ta dauki alhakin kisan, ta dora laifin afkuwar hakan akan kuskure.

Kuskuren harin jirgin sama mara matukin, wanda ya afku a ranar Lahadi, 3 ga watan Disambar daya gabata, yayi sanadiyar hallaka gwamman mutane tare da jikkata dimbin mazauna kauyukan Tudun Biri da Ugara da Sabon Gida bayan da suka taru domin gudanar da bikin Maulidi a garin Tudun Biri.

Da yake karin haske a yayin hirarsa da manema labaran, Manjo Janar Buba yace an mika rahoton binciken ga hukumomin da suka dace.

A watan Disambar da ya gabata ne Gwamnatin Najeriya ta fito karara ta ce za ta hukunta duk wanda ta samu da hannu a harin bam din matukar an gano akwai ganganci.

Ministan Labarun Najeriya Muhammad Idris Malagi ne ya ba da tabbacin a jawabinsa ga manema labaru na karshen shekarar 2023.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG