Wata kungiyar ma’aikatan man fetur a Nijeriya ta ce ta fara shirin daukar matakin farko na rufe ayyukan samar da danyan mai don ta nuna rashin amincewarta da tsananin tsadar mai.
Kungiyar PENGASSAN ta fadi jiya Laraba cewa mambobinta na kin tura bayanan aikin man ga jami’an gwamnati – wanda hakan shi ne mataki na farko na tsai da sarrafa danyan mai. Kungiyar ta ce ta umurci ma’aikatun mai su kasance a shirye don rufewa.
Rufe ma’aikatun mai zai durkusar da tattalin arzikin Nijeriya – kai ko barazanar yin hakan ka iya sa farashin mai ya tashi a kasuwannin duniya. Nijeriya dai na kan gaba wajen samar da mai a nahiyar Afirka kuma ta kan fitar da gangunan mai sama da miliyan biyu duk rana zuwa kasuwannin duniya.
Dubun dubatan ‘yan Nijeriya sun cigaba da zanga-zanga a rana ta uku zuwa jiya Laraba don nuna rashin amincewarsu da janye tallafin mai da gwamnati ta yi. Janye tallafin ya sa tsadar mai ta ninka tun bayan ranar zagayowar sabuwar shekara.
Kungiyoyin kwadago sun kaddamar da yajin aiki na sai baba ta gani. Gwamnati na barazanar kin biyan ma’aikatan da su ka ki komawa bakin aikinsu.
Shugabannin kungiyoyin na shawartar Shugaba Goodluck Jonathan cewa ya saurari jama’a. Shugaban kasar dai ya ki mayar da tallafin, ya na mai cewa gwamnati fa ba za ta iya ba.