Ana ta rawa a ko'ina a kan titunan kasar Zambia bayan da kungiyar 'yan wasan kwallon kafar kasar ta yi galaba akan 'yan wasan kasar Ivory Coast ko Cote d'Ivoire wadanda kowa ya baiwa nasara. 'Yan wasan Zambia sun yi nasara ne a bugun daga-kai-sai-gola bayan wasan karin lokaci.
'Yan kasar Zambia sun b'uge da murna lokacin da Stophria Sinzu ya huda raga da kwallon da ya ba su nasarar da ta kai su ga lashe kofin gasar kwallon kafar a jiya Lahadi a Libreville bayan sun doke Ivory Coast ko Cote d'Ivoire da ci takwas da bakwai.
Wannan ne kofin Zambia na farin farko a gasar kwallon kafar kasashen Afirka kuma nasara ce ta musamman mai tarin muhimmanci.
Daga isar su kasar Gabon a makon jiya domin buga wasan karshe, illahirin 'yan wasan na kasar Zambia sun kai ziyara bakin teku, kusa da inda hatsarin jirgin saman shekarar 1993 ya halaka duka 'yan wasan kasar 25 da ke cikin jirgin saman.