Takaddama tsakanin jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya da gwamnatin jahar Kaduna akan filin reshen Jami'ar da ke Mando a garin Kaduna dai, ta sa gwamnatin jahar rushe katangar jami'ar, abun da ya fusata ma'aikata da malamai su ka fara zanga-zanga.
Dafta Haruna Jibril shi ne shugaban kungiyar malamai ta ASUU, reshen Jami'ar ABU, kuma shi ya jagoranci zanga-zangar. Ya kuma ce an rusa bangon jami'ar da ke kare dalibai daga wasu matsaloli duk da kotu ta ba da umarnin kar a yi, su na kuma kiran hukumomin Jami'ar da su janye digirin El-Rufai saboda abubuwan da ya ke yi ba su dangaci wanda ya ke da shaidar takarda gama jami'ar ba.
Duk da nuna damuwar da jami'ar Ahmadu Bello ta yi dai gwamnatin jahar Kaduna ta ce ba ja-da-baya akan rushe gine-ginen da ta ce ba a yi su kan ka'ida ba, inji shugaban hukumar tsare-tsaren burane na jahar Kaduna wato KASUPDA, injiniya Ismail Umar Dikko.
Sai dai duk da wannan bayani, shugaban reshen Jami'ar ta Ahmadu Bello, Dafta Hassan Adamu Hamidu, ya ce gwamnatin Kaduna ta taka dokar kotu.
Shugaban hukumar tsare-tsaren buranen wato KASUPDA, injiniya Ismail Umar Dikko ya ce bai san wata maganar kotu ba.
Saurari cikakken rahoton cikin sauti: