Wani rahoto da kungiyar IPC, guda cikin kungiyoyin duniya da ke bincike a kan lamuran kiwon lafiya ya nuna yara ‘yan kasa da shekaru 5, miliyan 4 da dubu dari 4 ne suka fuskanci matsalar karanci abinci mai gina jiki a tsakanin watan Mayu na 2023 Afrilun bara, a wadannan shiyyoyi guda biyu.
Binciken ya haske cewa, raunin tattalin arzikin magidanta, hauhawar farashin kayayyaki da kuma kalubalen tsaro na cikin manyan dalilan da suka ta’azzara matsalar karancin abinci mai gina ciki, lamarin da ke barazana ga makomar lafiyar yaran.
Jihar Jigawa na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da wannan rahoto ya tabo, kuma hakan ba zai rasa nasaba da yunkurin da Ofishin maidakin gwamnan jihar, Amina Umar Namadi ke yi ba na bullo da wani shiri samar da abinci ga yara ‘yan kasa da shekaru 5 mai lakabin “Kwashpap”, inda har-ma aka tsara ba da horo na musamman ga mutane kimanin 600 a kan fasahar sarrafashi sinadarin abinci na yara.
A hira da Muryar Amurka, maidakin gwamnan na Jigawa, Amina Umar Namadi, ta ce “Kwashpap abinci yara ne da ake hada shi da waken Soya da Gyada da Alkama da Shinkafa ta Tuwa da kuma Jar Dawa wato (Kaura) kuma tuni aka kebe cibiyoyi guda 9 da za’a rinka koyar da wadannan mutane da aka zabo 600."
Ta ce "Gwamnati zata samar musu da kayayyakin aiki kuma ta saya bayan sun sarrafa domin rabawa a asibitocin ta da shagunan Kantin Sauki a garuruwa da kauyuka, a rinka bai wa iyaye mata kyauta”
A jihar Kano kuwa, kungiyar AD Rufa’i da ke ayyukan agaji dana kiwon lafiya ce ta ce, ta maida hankali a kan wayar da kan magidanta da iyaye mata game da hanyoyin magance matsalar karancin abinci ga yaran su kanana, a cewar Dr Musa Sufi jagoran kungiyar.
Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:
Dandalin Mu Tattauna