Fiye da mutane miliyan 40 ne ke shan bakar wahala kafin su samu abin da zasu ci a kasashen yammaci da tsakiyar Afirka bayan kakar 2024.
Sanarwar da shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya (WFP) ya fitar a yau Juma’a ta ce adadin na daf da karuwa zuwa mutane miliyan 52.7 nan da tsakiyar shekarar 2025, ciki har da mutane miliyan 3.4 dake fama da matsananciyar yunwa.
Da yake ruwaito sabon sharhin da ya fitar a kan samun wadatar abinci a wannan watan, WFP ya ce duk da dan ragin da aka samu a adadin mutanen da ke da matsananciyar bukatar abinci a bana ba kamar bara ba-hakan nada nasaba da ingantar tsaro da kuma samun damina mai kyau a wasu sassa na yankin sahel, har yanzu matsalar rashin wadatar abinci na kara ta’azzara.
Adadin mutanen da ke fama da matsananciyar yunwa ya karu da kaso 70 cikin 100 a lokacin kaka sannan da kaso 22 cikin 100 tsakanin farko da tsakiyar damina, a cewar sanarwar.
Kasashen da wannan matsala ta fi shafa sun hada da Najeriya da Kamaru da Chadi, wadanda gaba-dayansu suka samar da fiye da rabin adadin mutanen da basu da wadatar abinci-a yayin da ‘yan gudun hijira suka fi kowa shan wahalar matsalar karancin abincin.
Dandalin Mu Tattauna