Shugaba Akufo-Addo ya kafa wani kwamiti da zai tsara yadda za a biya matan shugabani. Ya ba da shawarar a sanya alawus a kan kudi daidai da na mataimakan minista amma za a dawo baya a fara biyan tun daga 2017.
Masu sukar sun ce wannan wani yunƙuri ne na ɓarnatar da dukiyar jama'a daga gwamnati wacce ta yi alkawarin kare dukiyar jama'a. Sun ce shugaban yana da albashi mai tsoka kuma zai ci gaba da karbar kudade har bayan ritaya, don haka babu bukatar a biya matar sa albashi.
Har ila yau, suna jayayya cewa tun da ba matan aka zaba kan Mulki ba ne, babu bukatar su karbi albashi. Sun kara da cewa biyan zai sabawa kundin tsarin mulki wanda bai tanadi albashi ga abokan huldar shugaban kasa da mataimakin sa ba.
Kafofin watsa labarai na kasar sun bayar da rahoton biyan kudi ga matan shugabanin har zuwa karshen shekarun 1990. Sai dai, wasu na cewa ya kamata ƙasar ta biya ƙarin kuɗi ga duk shugaba da ya kasance Musulmi kuma ya ke da mata huɗu.