Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotun Kolin Ghana Ta Tabbatar Da Sake Zaben Akufo-Addo


Nana Akufo-Addo
Nana Akufo-Addo

Yau Alhamis ne Cif Joji Kwasi Anin-Yeboah, da ya jagoranci rukunin alkalai bakwai na kotun kolin masu shari’a ne ya karanto hukuncin bai daya da alkalan suka zartar, wadanda suka fara sauraren kara kan zaben shugaban kasa tun daga ranar 14 ga watan Janairu 2021.

Babban alkalin (Cif Joji), ya ce tsohon shugaban John Dramani Mahama da ya shigar da karar bai gabatar da wata shaidar da zata kalubalanci sakamakon ba kamar yanda doka mai lamba CI135 ta gindaya, lamarin dake nuna yunkurin nashi bai yi tasiri ba.

“A kan haka ba mu da wani hurumi na bada umarnin sake shirya zabe kamar yanda mai kara ya shigar. Mun kuma yi fatali da karar a matsayin wacce ba ta da karfi,” inji Cif Joji a karshen jawabinsa na sa’o’i biyu kan hukuncin kotun kokin. Kotun dai ta ce mai shigar da karar ya gaza bada kwakkwarar hujja a kan bukatar da ya gabatar a kotun domin ta yanke hukunci a kai.

Toshon shugaban kasa John Dramani Mahama kuma dan takarar babbar jami’iyar hamayya ta National Democratic Congress (NDC) ne ya shigar da kara a kotun kolin. Mahama dai yana kalubalantar sakamakon zaben da hukumar zaben ta fitar a ranar tara ga watan Disamba, wanda ya ayyana sake zaben shugaba Akufo-Addo.

Mahama ya kai karar hukumar zabe da shugaba Akufo-Addo kotun koli, a matsayin masu amsa kara na daya da na biyu.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG