Sai dai manazarta na nuna shakkun yadda za a gudanar da zaben kasa tare da kidayar a kusan lokaci daya duk da rashin tsaron da kasar ke fuskanta.
Tun shekara ta 2006 ne aka gudanar da kidayar al'umma a Najeriya.
A shekaru 16 din nan kiyasi ake yi na yawan al'umman kasar da cewa sun kai Miliyan dari biyu da kusan goma sha daya, amma Shugaban Hukumar NPC, Nasir Isa Kwarra, ya ce hukumar ta shirya tsaf wajen sake rubuta tarihin kidayar jama'a a Najeriya ta yin amfani da fasahar zamani.
Nasir ya ce kidayar abu ce mai matukar muhimmanci ga al'ummar kasar, kuma ta hanyar kidayar jama'a ana samar da bayanan da za a yi amfani da su wajen tsara manufofi don ci gaba ta matakai uku na gwamnati, wato kananan hukumomi, jihohi da kuma matakan Gwamnatin taraiyya,har da Kamfanoni masu zaman kansu duksuna bukatar alkaluman.
Shi kuwa mai nazari a fannin tsaro, Dokta Yahuza Ahmed Getso, yana mai ra'ayin cewa halin rashin tsaro da kasa ke fama da shi zai sa ba za a iya samun isa wasu wurare ba, sai dai idan hukumar za ta bada tabbacin cewa akwai wata hanya da za ta yi amfani da ita wajen fitar da sahihin alkalumar kidayyar.
To sai dai Shugaban Kwamitin Kula da Kidayar Jama'a a Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Sahabi Ya'u Kaura, ya yi nazari cewa an riga an yi gwajin kidayar, kuma yayi armashi kwarai da gaske.
Sahabi ya ce duk gidajen da ke Najeriya hukumar ta riga ta san da zaman su, kuma suna da hotunan su. Ya ce wannan kidaya ba irin wadda aka yi a shekaru 16 da suka wuce ba ne, wanan kidaya ta kimiya ce.
Sahabi ya yi wa hukumar alkawalin majalisar dattawa za ta tabbatar cewa hukumar ta samu dukan kudaden da take bukata, wajen yin wannan aiki na kidayar al'umman Najeriya, da zai lakume Naira Biliyan 532.7.
Saurari cikakken rahoton Medina Dauda: